AroundMaps Logo
Search
Add Listing

Jibwis Gabasawa Lg Kano State Nigeria

0

About Jibwis Gabasawa Lg Kano State Nigeria

Sunnah sak Bid'ah sam

Tags

Map

Item Reviews - 6

Anynomous

"

*💌KUNDIN MA'AURATA //38💞*

MATA BA SA GANEWA NE

Babban abin da namiji yake tunani shi ne yadda tsadar rayuwa ta dabaibaye maza a maraya, masamman abin da ya shafi kudin haya, tsadar abinci, kudin makaranta, da sauran al'amura na yau da kullum, da zarar an ce yara za su fara jarabawa uwayensu za su fara tunanin kudin makarantarsu in sun dawo hutu, kenan duk wanda zai yi aure dole ya duba wadannan sassan guda uku, in dai mutum ya ce zai auri bazawara a yau, kuma ya ce ba ya buqa...

Continue Reading "

25 June 2023

Anynomous

"

KADA KA JI KUNYAR SANA'ARKA

In na ga matashi mai jini a jika da cikakken lafiya ya yi abota da dabar shan inuwa, ya auri katifarsa, sannan ya kurɓi ruwan kasala da ta lalata masa tunaninsa da zuciyarsa sai ya bani tausayi wallahi. Domin bai taimaki kansa ko addininsa ba, musuluncin mu bai yarda da maula da rashin zuciya da neman na kai ba.

Kana zaune duk samarin unguwarku sun fita nema. Kai kana kwance a katifarka, da yammaci suna ta komowa gida da ƴan kwabbansu a aljihu, kai... kuma kana zaune a majalisar ƴan sa idon unguwa da zagin jama'a. 🙄 Ka fi kowa iya gardama a majalisa, in wannan mutumin ya wuce ka zage shi, in wancan ya wuce da babban mota a ce masa ɓarawo. To in shi ɓarawo ne kai kuma ina naka sana'ar?

Da zaman banzan nan ina ma rake ka fara siyarwa a kofar gidanku, ina ma saro mangoro ka yi da abarba da lemo. Kai ko shoeshiner ka zama ya fi zaman banza. Domin in zaman banza yayi yawa, sai kaucewar hankali ya shigo. Ka ga mutum ya faɗa shaye-shayen da ɗauke-ɗauke, ko ma manyan zunuban da suka fi wannan.

Kana kunyar sana'arka? Ko kuwa a'a saboda budurwarka ce? Kana ganin zata raina maka hanyar cin abincinka? In ka yi haka baka kyauta ba sam wallahi. In zata so ka to ta so sana'arka muddin bana sabon Allah bane. In ta raina maka je ka nemi wacce zata yi alfahari da kai, wacce kullum zata ƙarfafaka, ka wuce in da kake. Kada ka duba me dangi zasu ce ko abokanka domin duk abun da ka yi ba zaka burge mutane ba. Barsu su raina sana'arka wata rana sai sun wayi gari ka musu nisa, kuma sai sun zo neman taimako wurinka.

Kada ka ji kunyar sana'arka komin ƙanƙantarta domin ta fi ka yi sata. Idan har baka mallaki abun nemanka ba to ba zaka mallaki maganarka ba. Kwaɗayi da bin wani ya baka yana mutuƙar kashewa matashi zuciyarsa. Kada ka je kana ma wani maula kullum, a'a roƙe shi ya nuna maka hanyar da kai ma zaka nemi naka. Sannan kada ka raina ƙanƙanin abun da yake zuwan maka domin da kaɗan ake tara mai yawa. Matasan mu burinsu su yi kuɗi yanzu-yanzu, shi yasa sai ya raina hanyar samunsa. Ko mutum ya faɗa sana'ar da zata kawo masa kuɗi ba tare da ya sha wuya ko yayi shekaru yana jiran zuwan su ba. Ka bincika duka masu kuɗin duniya ka ga ta yanda suka fara. Don Allah kada ka cire rai ga samun arziƙi domin na Allah ne bana wani ba. Ka yi addu'a kuma ka nema, nema mai yawa.

Har yau kana kwance a ɗaki ko? Kuma kana son ka yi aure, kana son ka ji daɗi ka kashe kudi. 🙂 kuɗi ba sa zuwa su sami mutum a katifarsa. Kada ka tsaya bata lokaci wurin yi ma wani hassada ko bakin ciki. A'a tashi ka nemi naka kai ma sai ka kauce ma bakin cikin.

Mai nema yana tare da samu, kuma ko bai samu ba to dai ya wuce wulaƙancin mai wulaƙanci.

Yaa Allah Ka kare mu daga mugun talauci, Ka azurta mu da halali mai yawa. Ka kuma bamu ikon jin daɗi da kashe su ta hanyar da ta dace.

See More "

17 March 2023

Anynomous

"

Assalamu alaikum warahamatullah,

*Muna masu farin cikin sanar da Dalibai da yan'uwa musulmi baki 1 cewar ga sabon Page na Facebook na babban Malamin mu.*

*Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib.*

...

*Insha Allah zai dunga kawo muku karatuttakan Malam kai tsaye da yardar Allah.*

Idan komai ya kan kama zamu sanar.

*Zaku iya like idan kuka danna wannan bulun rubutun na kasa.* ߑǰߏ늨ttps://www.facebook.com/Sheikhlawanabubakarshuaib/

*Kayi addu'a a zuciyar ka /ki.*

See More "

26 December 2023

Anynomous

"

WASIYYA MAI MATUKAR AMFANI GA 'YAN UWA MUSULMAI _______________________________________________

وصية سفيان الثوري رحمه الله

...

من وصية سفيان الثوري لعلي بن الحسن السلمي ليكن جليسك من يزهدك في الدنياء ويرغبك في الاخره وإياك ومجالسة أهل الدنيا الذين يخوضون في حديث الدنيا فإنهم يفسدون عليك دنياك وقلبك وأكثر ذكر الموت وأكثر الاستغفار مما قد سلف من ذنوبك وسل الله السلامة لما بقي من عمرك.

المصدر حلية الأولياء (7/82)

Wasiyyar Sufyanus Saureey (Allah masa Rahma)

Daga cikin Wasiyyan Sufyanus Saureey ga Ali Bin Hassan Assulameey, ya kasance abokin zaman ka wanda yake gudun duniya kuma yana kwadayin lahira kuma kashe-dinka ga ma'abota duniya (masu son duniya) wa 'yanda suke kutsawa cikin labarin duniya, domin su, zasu 6ata maka duniyan ka da zuciyan ka kuma ka yawaita tuna mutuwa da yin istigfari ga abinda ya wuce daga cikin zunuban ka kuma ka roke Allah aminci da abinda ya rage na sauran shekarun ka.

Madora : [Hilyatil Auliyaa'i (7/82)]

ALLAHU'AKBAR wasiyya mai ratsa jiki ga mai neman sanin addini da shiriya.

See More "

25 December 2023

Anynomous

"

illar Darikar Tijjaniyya ''' Ahmadu Tijjani yache duk wanda yaganshi a mafarki Ranar Litinin ko juma'a tozai shiga Aljannah ba tare da Hisabi ba 'kaduba Jawahirul ma'ani (Vol 1 page 133) //har ila yau Mabiya Darikar Tijjani sunche Annabi baiyiwa... Sahabbanshi Adalchiba saboda yaki basu dama su fara yin Darika sai Bayan shekara 1150 wai ya taso daga Kabarinsa a Madina Yazo birnin Fez yaba Ahmadu Tijjani wannan Darikar duba Jawahirul ma'ani (vol 1 page 52) achikin wannan littafin na Jawahirul Ma'ani anfadi Ranar da aka Haifi shi Tijjanin Anhaifeshi ne Bayan Rasuwar Annabi s'a'w da shekara 1150 a garin aina Mali dake kasar Morocco // sannan sukache akwai wani zikiri wanda idan kayi za'a baka Ladan Annabawa 70 wadanda suka isar da sakon Allah duba Jawahirul Ma'ani (Vol 1 page 136) kuma Wallahi babu Qarya achiki

See More "

13 December 2023

Anynomous

"

GA WASU HANYOYI GUDA SHIDA WADANDA ZAKA IYA BINSU DON GYARA HALAYENKA :

1. Cikakken imani na gaskiya tare da yawaita neman kusanci da Allah ta hanyar aikata dukkan abinda zai janyo kusancinka dashi. Ta hanyar kwatanta yin haka ne zuciya take samun kaifi, Kuma mutum yake samun saukin suluki (tafiya) bisa hanyar neman yardar Ubangijinsa.

2. - Zama tare da kulla abota da mutanen kirki masu kyawawan halaye. Domin kuwa abokai suna taka muhimmiyar rawa acikin tarbiyyar abokansu ta... fuskar Mu'amala da kuma zama yau da kullum.

Shi yasa malamai suka ce ''Shi aboki mai jan abokinsa ne. Idan shi na kirki ne zai jashi zuwa alkhairi. Idan kuma shi na banza ne, to zai ja abokinsa ne zuwa ga sharri.

Wani Malami ya fa'da acikin waqa : "Kar ka tambaya game da halin mutum, Kai dai ka tambayi su waye abokansa?. Domin kowanne aboki yana koyi ne da abokansa".

3. Hanya ta uku ita ce : Ka rika yiwa kanka hisabi domin ita zuciya bisa hakikanin gaskiya an halicceta ne bisa dabi'ar yin umurni da munanan abubuwa. Kuma ita zuciya kullum kokarinta shine ta jaka zuwa ga sharri.

Don haka ka rika tuhumar zuciyarka kana yi mata hisabi kuma kana janta zuwa ga alkhairi. Kar ka zama mai binta duk inda ta jaka kamar jela, tana janka zuwa ga bin son ranta.

Imam Busiriy yace "Ita zuciya kamar Jariri take. Domin shi jariri idan ka kyaleshi kaci gaba da shayar dashi, sai ya girma bai dena son shan nono ba. Amma idan ka yayeshi shikenan sai ya yayu".

4. Na hudu shine : Ka yawaita jarraba aiki da kyawawan halaye madaukaka irin su Hakuri, juriya, Tawadhu'u, kyauta, biyayya, gaskiya, amana, sakin fuska, etc.

Alokaci guda kuma ka rika kokarin kauce ma miyagun halaye irin su Qarya, girman kai, rowa, ha'inci, taurin kai, riko, gaaba, hassada, etc.

Shi yasa Manzon Allah (saww) yace : "SHI ILIMI ANA SAMUNSA NE DA NEMAN ILIMI. SHI KUMA HAKURI DA HAKURKURTAR DA RAI".

5. Hanya ta biyar ita ce: Ka rika karanta tarihin magabata na kwarai kana jin yadda sukayi rayuwarsu cikin neman yardar Allah da guje ma sa'ba masa.

Domin karanta tarihinsu wata babbar hanya ce muhimmiya ta gyaran halaye domin zaka ji labari daga manyan Maluma wanda acikinsa zaka ji yadda halayensu da ladubansu yake.

6. Hanya ta shida ita ce: ka rika rokon Allah cewa ya baka kyawawan halaye, kuma ya rabaka da miyagun halayen dake tare da kai.

Yin wannan yana daga cikin manyan hanyoyin da zasu kaika zuwa ga kyautatuwar halaye.

Daga cikin addu'o'in da Manzon Allah (saww) yake yi akwai wacce yake cewa:

"YA ALLAH KA SHIRYAR DANI ZUWA GA MAFI KYAWUN HALAYE. DOMIN BABU MAI SHIRYARWA ZUWA GA MAFI KYAWUNTA SAI DAI KAI.

"KUMA KA JUYAR DA MAFIYA MUNINTA DAGA GARENI. DOMIN BABU MAI JUYARWA DAGA MAFI MUNINTA SAI DAI KAI".

Ya Allah muna Tawassuli da mafi kyawun halaye da dabi'u acikin bayinka don alfarmarsa ka kyautata halayenmu. Ka kiyayemu daga miyagun halaye.

See More "

21 September 2023

Add Reviews & Rate item

Your rating for this listing :

Help Us to Improve :

Location / Contacts :